ABNA24 : Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne daga tsakar daren jiya Lahadi zuwa safiyar yau Litinin inda mutane suka ce sun ji ƙarar bindigogi da fashe-fashen abubuwan fashewa a lokacin da maharan suke kai harin.
Har ya zuwa yanzu dai ba a tantance ko su wa suka kai harin ba sai dai kuma ana nuna yatsar zargi ga 'yan haramtacciyar ƙungiyar nan ta IPOB ta Inyamurai masu son ballewa daga Nijeriyan. An ce fursunoni da dama ne suka gudu yayin da aka kai hari gidan yarin na Owerri duk da cewa wasu rahotannin sun ce wasu fursunonin da suka gudun sun dawo, wasu kuma sun ƙi amincewa su gudun ma. Har yanzu dai ba a tantance adadin fursunonin da suka gudu daga gidan yarin da aka ce yana ɗauke da frusunoni 2,156 maimakon 548 da aka gina shi don ya ɗauke su.
Hotunann da aka fitar dai suna nuni da irin ɓarnar da maharar suka haifar wa helkwatar ‘yan sandan da kuma gidan yarin.
A makon da ya wuce dai rundunar ‘yan sandan jihar Imo ɗin ta kama mutane da dama da take zargin suna daga cikin waɗanda suke kai wa ‘yan sandan da kuma ofisoshinsu hare-hare da yayi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaron da dama. Wasu suna alaƙanta wannan harin na yau da waɗancan kame-kamen da aka yi.
342/